2 'Ya'yan Yafet ke nan, da Gomer, da Magog, da Madai, da Yawan, da Tubal, da Meshek, da Tiras.
3 'Ya'yan Gomer kuma Ashkenaz, da Rifat, da Togarma.
4 'Ya'yan Yawan kuma Elisha, da Tarshish, da Kittim, da Rodanim.
5 Daga waɗannan ne mazauna a bakin gāɓa suka yaɗu bisa ga ƙasashensu, kowanne da harshensa, bisa ga iyalansu da kabilansu.
6 'Ya'yan Ham su ne Kush, da Mizrayim, da Fut, da Kan'ana.
7 'Ya'yan Kush kuma Seba, da Hawila, da Sabta, da Ra'ama, da Sabteka. 'Ya'yan Ra'ama kuwa Sheba da Dedan.
8 Kush ya haifi Lamirudu, shi ne mutumin da ya fara ƙasaita cikin duniya.