1 A lokacin, harshen mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.
2 Sa'ad da mutane suke ta yin ƙaura daga gabas, sai suka sami fili a ƙasar Shinar, suka zauna a can.
3 Sai suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi aiki da tubali maimakon dutse, katsi kuma maimakon lāka.
4 Sai suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni, da hasumiya wadda ƙwanƙolinta zai kai can cikin sammai domin mu yi wa kanmu suna, domin kada mu warwatsu ko'ina bisa duniya.”
5 Ubangiji kuwa ya sauko ya ga birnin da hasumiyar da 'yan adam suka gina.
6 Ubangiji kuwa ya ce, “Ga su, su jama'a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne, to fa, ga irin abin da suka fara yi, ba abin da za su shawarta su yi da zai gagare su.
7 Zo mu sauka, mu dagula harshensu, domin kada su fahimci maganar juna.”