10 Waɗannan su ne zuriyar Shem. Lokacin da Shem yake da shekara ɗari, ya haifi Arfakshad bayan Ruwan Tsufana da shekara biyu.
11 Shem kuwa ya yi shekara ɗari biyar bayan haihuwar Arfakshad, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
12 Sa'ad da Arfakshad yake da shekara talatin da biyar ya haifi Shela.
13 Arfakshad kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Shela, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
14 Sa'ad da Shela yake da shekara talatin, ya haifi Eber,
15 Shela kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Eber, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
16 Sa'ad da Eber ya yi shekara talatin da huɗu ya haifi Feleg,