15 Da fādawan Fir'auna suka gan ta, sai suka yabe ta a gaban Fir'auna. Aka ɗauke ta aka kai ta gidan Fir'auna.
16 Saboda ita Fir'auna ya yi wa Abram alheri. Abram yana da tumaki, da takarkarai, da jakai maza, da barori mata da maza, da jakai mata, da raƙuma.
17 Sai Ubangiji ya wahalar da Fir'auna da gidansa da manya manyan annobai saboda matar Abram, Saraya.
18 Sai Fir'auna ya kirawo Abram, ya ce, “Mene ne wannan da ka yi mini? Don me ba ka faɗa mini ita matarka ce ba?
19 Don me ka ce ita 'yar'uwarka ce, har na ɗauke ta ta zama matata? To, ga matarka, ka ɗauke ta ka tafi.”
20 Fir'auna kuma ya umarci mutanensa a kan Abram, su raka shi da matarsa, da dukan abin da yake da shi.