3 Ya yi ta tafiya daga Negeb har zuwa Betel, har wurin da ya kafa alfarwarsa da fari, tsakanin Betel da Ai,
4 a inda dā ya gina bagade. A can Abram ya kira bisa sunan Ubangiji.
5 Lutu wanda ya tafi tare da Abram, shi kuma yana da garkunan tumaki, da na shanu, da alfarwai,
6 domin haka ƙasar ba ta isa dukansu biyu su zauna tare ba, saboda mallakarsu ta cika yawa, har da ba za su iya zama tare ba.
7 Akwai rashin jituwa kuma a tsakanin makiyayan dabbobin Abram da makiyayan dabbobin Lutu. Mazaunan ƙasar, a lokacin nan Kan'aniyawa da Ferizziyawa ne.
8 Abram ya ce wa Lutu, “Kada rashin jituwa ya shiga tsakanina da kai ko tsakanin makiyayanka da nawa, gama mu 'yan'uwa ne.
9 Ba ƙasar duka tana gabanka ba? Sai ka ware daga gare ni. In ka ɗauki hagu in ɗauki dama, in kuwa ka ɗauki dama ni sai in ɗauki hagu.”