14 Lokacin da Abram ya ji an kama danginsa wurin yaƙi sai ya shugabanci horarrun mutanensa, haifaffun gidansa, su ɗari uku da goma sha takwas, suka bi sawun sarakunan har zuwa Dan.
15 Da dad dare sai ya kasa jarumawansa yadda za su gabza da su, shi da barorinsa, ya kuma ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewacin Dimashƙu.
16 Sai ya washe kayayyakin duka, ya kuma ƙwato ɗan'uwansa Lutu da kayayyakinsa da mata da maza.
17 Sai Sarkin Saduma ya fita ya taryi Abram sa'ad da ya komo daga korar Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi, a Kwarin Shawe, wato Kwarin Sarki.
18 Sai Malkisadik Sarkin Salem, wato Urushalima, ya kawo gurasa da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Maɗaukaki.
19 Ya kuwa sa wa Abram albarka ya ce, “Shi wanda ya yi sama da ƙasa, Allah Maɗaukaki ya sa wa Abram albarka.
20 Ga Allah Maɗaukaki yabo ya tabbata, shi wanda ya ba ka maƙiyanka a tafin hannunka!” Abram kuwa ya ba shi ushiri na duka.