6 da kuma Horiyawa cikin dutsen nan nasu, wato Seyir, har zuwa Elfaran a bakin jeji.
7 Sai suka juya suka je Enmishfat, wato Kadesh, suka kuwa cinye ƙasar Amalekawa da kuma ta Amoriyawa waɗanda suka zauna cikin Hazazontamar.
8-9 Sai Sarkin Saduma, da Sarkin Gwamrata, da Sarkin Adma da Sarkin Zeboyim, da Sarkin Bela, wato Zowar, suka fita suka ja dāga da Kedarlayomer Sarkin Elam, da Tidal Sarkin Goyim, da Amrafel Sarkin Shinar, da Ariyok Sarkin Ellasar a kwarin Siddim, sarakuna huɗu gāba da biyar.
10 Akwai ramummukan kalo da yawa a kwarin Siddim. Da Sarkin Saduma da na Gwamrata suka sheƙa da gudu sai waɗansunsu suka fāɗa cikin ramummukan, sauran kuwa suka gudu zuwa dutsen.
11 Sai abokan gāba suka kwashe dukan kayayyakin Saduma da na Gwamrata, da abincinsu duka, suka yi tafiyarsu.
12 Suka kuma kama Lutu ɗan ɗan'uwan Abram, wanda yake zaune a Saduma, da kayayyakinsa, suka yi tafiyarsu.
13 Sai wani da ya tsere, ya zo ya faɗa wa Abram Ba'ibrane wanda yake zaune wajen itatuwan oak na Mamre, Ba'amore, ɗan'uwan Eshkol da Aner, waɗanda suke abuta da Abram.