15 Kai kuwa, cikin salama za ka koma ga iyayenka, da kyakkyawan tsufa za a binne ka.
16 A tsara ta huɗu kuma, zuriyar za ta komo nan, domin adadin muguntar Amoriyawa bai cika ya kai iyaka ba tukuna.”
17 Sa'ad da rana ta fāɗi aka kuwa yi duhu, sai ga tanderun wuta mai hayaƙi da jiniya mai harshen wuta suka ratsa tsakanin abubuwan nan da aka tsattsaga a tsaka.
18 A wannan rana Ubangiji ya yi wa Abram alkawari ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis ke nan,
19 ƙasar Keniyawa, da Kenizziyawa, da Kadmoniyawa,
20 da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Refayawa,
21 da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Girgashiyawa, da kuma Yebusiyawa.”