13 Sai ta kira sunan Ubangiji wanda ya yi magana da ita, “Kai Allah ne mai gani,” gama ta ce, “Ni! Har na iya ganin Allah in rayu?”
14 Domin haka aka kira sunan rijiyar, Biyer-lahai-royi, tana nan tsakanin Kadesh da Bered.
15 Hajaratu ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya sa wa ɗa da Hajaratu ta haifa suna, Isma'ilu.
16 Abram yana da shekara tamanin da shida sa'ad da Hajaratu ta haifa masa Isma'ilu.