1 Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ibrahim kusa da itatuwan oak na Mamre, a lokacin da yake zaune a ƙofar alfarwarsa da tsakar rana.
2 Da ya ɗaga idonsa, ya duba sai ga mutum uku suna tsaye a gabansa. Da ya gan su, sai ya sheƙa da gudu daga ƙofar alfarwar, don ya tarye su. Ya yi ruku'u,
3 ya ce, “Ya Ubangiji, in na sami tagomashi a gabanka, kada ka wuce gidana. A shirye nake in yi muku hidima.
4 Bari a kawo ɗan ruwa ku wanke ƙafafunku, ku shaƙata a gindin itace,
5 ni kuwa in tafi in kawo ɗan abinci, don rayukanku su wartsake, bayan haka sai ku wuce, tun da yake kun biyo ta wurin baranku.”Sai suka ce, “Madalla! Ka aikata bisa ga faɗarka.”
6 Ibrahim kuwa ya gaggauta zuwa cikin alfarwa wurin Saratu, ya ce, “Ki shirya mudu uku na gari mai laushi da sauri, ki cuɗa, ki yi waina.”