1 Mala'ikun nan biyu kuwa suka isa Saduma da maraice, Lutu kuwa yana zaune a ƙofar Saduma. Sa'ad da Lutu ya gan su sai ya miƙe ya tarye su. Sai ya yi ruku'u a gabansu.
2 ya ce, “Iyayengijina, ina roƙonku ku ratse zuwa gidan baranku, ku kwana, ku wanke ƙafafunku, da sassafe kuma sai ku kama hanyarku.”Suka ce, “A'a, a titi za mu kwana.”
3 Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka ratse suka shiga gidansa, ya shirya musu liyafa, ya toya musu abinci marar yisti, suka ci.
4 Amma kafin su shiga barci, mutanen birnin Saduma, samari da tsofaffi, dukan mutane gaba ɗaya suka kewaye gidan.
5 Suka kira Lutu suka ce, “Ina mutanen da suka zo wurinka da daren nan? Fito mana da su waje, don mu yi luɗu da su.”
6 Lutu ya fita daga cikin gida ya rufe ƙofar a bayansa ya je wurin mutane,