7 Yanzu fa, sai ka mayar wa mutumin da matarsa, gama shi annabi ne, zai yi maka addu'a, za ka kuwa rayu. In kuwa ba ka mayar da ita ba, ka sani hakika za ka mutu, kai, da dukan abin da yake naka.”
8 Abimelek ya tashi da sassafe, ya kira barorinsa duka ya kuma faɗa musu waɗannan abubuwa duka. Mutanen kuwa suka ji tsoro ƙwarai.
9 Abimelek kuwa ya kira Ibrahim, ya ce masa, “Me ke nan ka yi mana? Wane laifi na yi maka, da za ka jawo bala'i mai girma haka a kaina da mulkina? Ka yi mini abin da bai kamata a yi ba.”
10 Abimelek kuma ya ce wa Ibrahim, “Me ya sa ka yi wannan abu?”
11 Ibrahim ya ce, “Na yi haka, domin ina zaton babu tsoron Allah ko kaɗan a wannan wuri, shi ya sa na zaci, kashe ni za a yi saboda matata.
12 Banda haka nan ma, hakika ita 'yar'uwata ce, 'yar mahaifina amma ba ta mahaifiyata ba ce. Na kuwa aure ta.
13 A lokacin da Allah ya raba ni da gidan mahaifina, ya sa ni yawace yawace, na ce mata, ‘Wannan shi ne alherin da za ki yi mini a duk inda muka je, ki ce da ni ɗan'uwanki ne.’ ”