8 Abimelek ya tashi da sassafe, ya kira barorinsa duka ya kuma faɗa musu waɗannan abubuwa duka. Mutanen kuwa suka ji tsoro ƙwarai.
9 Abimelek kuwa ya kira Ibrahim, ya ce masa, “Me ke nan ka yi mana? Wane laifi na yi maka, da za ka jawo bala'i mai girma haka a kaina da mulkina? Ka yi mini abin da bai kamata a yi ba.”
10 Abimelek kuma ya ce wa Ibrahim, “Me ya sa ka yi wannan abu?”
11 Ibrahim ya ce, “Na yi haka, domin ina zaton babu tsoron Allah ko kaɗan a wannan wuri, shi ya sa na zaci, kashe ni za a yi saboda matata.
12 Banda haka nan ma, hakika ita 'yar'uwata ce, 'yar mahaifina amma ba ta mahaifiyata ba ce. Na kuwa aure ta.
13 A lokacin da Allah ya raba ni da gidan mahaifina, ya sa ni yawace yawace, na ce mata, ‘Wannan shi ne alherin da za ki yi mini a duk inda muka je, ki ce da ni ɗan'uwanki ne.’ ”
14 Abimelek ya ɗauki tumaki da takarkarai, da bayi mata da maza, ya ba Ibrahim, ya kuma mayar masa da matarsa Saratu.