50 Laban da Betuwel suka amsa suka ce, “Wannan al'amari daga Ubangiji ne, ba mu da iko mu ce maka i, ko a'a.
51 Ga Rifkatu nan gabanka, ka ɗauke ta ku tafi, ta zama matar ɗan maigidanka, bisa ga faɗar Ubangiji.”
52 Sa'ad da baran Ibrahim ya ji wannan, ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya yi sujada a gaban Ubangiji.
53 Sai baran ya kawo kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, ya bai wa Rifkatu, ya kuma ba ɗan'uwanta da mahaifiyarta kayan ado masu tsada.
54 Shi da mutanen da suke tare da shi suka ci suka sha, suka kwana wurin. Da suka tashi da safe, sai ya ce, “A sallame ni, in koma wurin maigidana.”
55 Ɗan'uwanta da mahaifiyarta suka ce, “Ka bar budurwar tare da mu har ɗan lokaci, kada ya gaza kwana goma, bayan wannan ta tafi.”
56 Amma ya ce musu, “Kada ku makarar da ni, tun da yake Allah ya arzuta tafiyata, a sallame ni domin in koma wurin maigidana.”