57 Suka ce, “Za mu kira budurwar mu tambaye ta.”
58 Suka kirawo Rifkatu suka ce mata, “Za ki tafi tare da wannan mutum?”Sai ta ce, “Zan tafi.”
59 Suka kuwa sallami Rifkatu 'yar'uwarsu da uwar goyonta, da baran Ibrahim da mutanensa.
60 Suka sa wa Rifkatu albarka, suka ce mata,“'Yar'uwarmu, ki zama mahaifiyardubbai,Har dubbai goma,Bari zuriyarki kuma su gāji ƙofofinmaƙiyansu!”
61 Sai Rifkatu da kuyanginta suka tashi suka hau raƙuman, suka bi mutumin. Haka nan kuwa baran ya ɗauki Rifkatu ya koma.
62 A lokacin kuwa Ishaku ya riga ya zo daga Biyer-lahai-royi yana zaune a Negeb.
63 A gabatowar maraice, sai Ishaku ya fita saura ya yi tunani, ya ɗaga idanunsa ya duba, ya ga raƙuma suna zuwa.