8 Amma idan matar ba ta yarda ta biyo ka ba, ka kuɓuta daga rantsuwan nan tawa. Kai dai kada ka koma da ɗana can.”
9 Sai baran ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyar Ibrahim maigidansa, ya kuwa rantse masa zai yi.
10 Baran ya ɗibi raƙuma goma daga cikin raƙuman maigidansa. Ya tashi, yana ɗauke da tsaraba ta kowane irin abu mai kyau na maigidansa a hannunsa. Ya kama hanyar Mesofotamiya zuwa birnin Nahor.
11 Ya durƙusar da raƙumansa a bayan birnin, kusa da bakin rijiyar ruwa da maraice, wato lokacin da mata sukan tafi ɗebo ruwa.
12 Sai ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim.
13 Ga shi kuwa, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa, ga kuma 'yan matan mutanen birnin suna fitowa garin ɗibar ruwa.
14 Bari budurwar da zan ce wa, ‘Ina roƙo, ki sauke tulunki domin in sha,’ wadda za ta ce, ‘Sha, zan kuma shayar da raƙumanka,’ bari ta zama ita ce wadda ka zaɓa wa baranka Ishaku. Ta haka zan sani ka nuna madawwamiyar ƙaunarka ga maigidana.”