11 Abimelek ya umarci dukan mutane ya ce, “Duk wanda ya taɓa mutumin nan ko matarsa, za a kashe shi.”
12 Ishaku ya yi shuka a waccan ƙasar, a shekaran nan kuwa ya girbe cikakken amfani. Ubangiji ya sa masa albarka,
13 har mutumin ya arzuta, ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri.
14 Da yake ya yi ta arzuta da garken tumaki, da na shanu, da iyali masu yawa, Filistiyawa suka ji ƙyashinsa.
15 Saboda haka, Filistiyawa don kishi sai suka ciccike rijiyoyin da ƙasa, waɗanda barorin mahaifinsa, Ibrahim, suka haƙa tun Ibrahim yana da rai.
16 Abimelek kuwa ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu, gama ka fi ƙarfinmu.”
17 Don haka Ishaku ya bar wurin, ya yi zango cikin kwarin Gerar, ya yi zamansa a can.