13 har mutumin ya arzuta, ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri.
14 Da yake ya yi ta arzuta da garken tumaki, da na shanu, da iyali masu yawa, Filistiyawa suka ji ƙyashinsa.
15 Saboda haka, Filistiyawa don kishi sai suka ciccike rijiyoyin da ƙasa, waɗanda barorin mahaifinsa, Ibrahim, suka haƙa tun Ibrahim yana da rai.
16 Abimelek kuwa ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu, gama ka fi ƙarfinmu.”
17 Don haka Ishaku ya bar wurin, ya yi zango cikin kwarin Gerar, ya yi zamansa a can.
18 Sai Ishaku ya sāke haƙa rijiyoyi waɗanda dā aka haƙa a zamanin Ibrahim mahaifinsa, gama Filistiyawa sun tattoshe su bayan rasuwar Ibrahim. Ishaku kuma ya sa wa rijiyoyin sunayen da mahaifinsa ya sa musu.
19 Amma sa'ad da barorin Ishaku suka haƙa rijiya a kwarin, sai suka tarar da idon ruwa.