8 Sa'ad da ya dakata 'yan kwanaki a can, sai Abimelek, Sarkin Filistiyawa ya duba ta taga, ya ga Ishaku ya rungumi Rifkatu.
9 Sai Abimelek ya kira Ishaku, ya ce, “Ashe lalle ita matarka ce, ƙaƙa fa ka ce, ‘Ita 'yar'uwata ce’?”Ishaku ya amsa masa ya ce, “Don na yi tsammani zan rasa raina saboda ita.”
10 Abimelek ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Ai, da wani daga jama'a ya kwana da matarka a sawwaƙe, da ka jawo laifi a bisanmu.”
11 Abimelek ya umarci dukan mutane ya ce, “Duk wanda ya taɓa mutumin nan ko matarsa, za a kashe shi.”
12 Ishaku ya yi shuka a waccan ƙasar, a shekaran nan kuwa ya girbe cikakken amfani. Ubangiji ya sa masa albarka,
13 har mutumin ya arzuta, ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri.
14 Da yake ya yi ta arzuta da garken tumaki, da na shanu, da iyali masu yawa, Filistiyawa suka ji ƙyashinsa.