1 Yakubu kuwa ya ci gaba da tafiyarsa, har ya kai ƙasar Mesofotamiya.
2 Da ya duba haka sai ya ga rijiya cikin saura, ga kuwa garken tumaki uku suna daura da ita, gama daga cikin rijiyar nan ake shayar da garkunan. Murfin rijiyar, dutse ne, babba.
3 A sa'ad da garkunan suka tattaru a wurin, makiyayan sukan kawar da dutsen daga bakin rijiyar, su shayar da su, sa'an nan su mayar da dutsen a wurinsa, a bisa bakin rijiya.
4 Yakubu ya ce musu, “'Yan'uwana, daga ina kuka fito?”Suka ce, “Daga Haran muke.”