1 Maciji ya fi kowace dabba da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa matar, “Ko Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga wani itacen da yake a gonar ba?’ ”
2 Sai matar ta ce wa macijin, “Mā iya ci daga cikin itatuwan gonar,
3 amma Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga cikin 'ya'yan itacen da yake tsakiyar gonar ba, ba za ku taɓa shi ba, don kada ku mutu.’ ”
4 Amma macijin ya ce wa matar, “Hakika ba za ku mutu ba.