16 Sa'ad da Yakubu ya komo daga saura da maraice, Lai'atu ta fita ta tarye shi, ta ce, “Sai ka shigo wurina, gama na riga na ijarar da kai da manta uwar da ɗana ya samo.” Saboda haka ya kwana tare da ita a daren nan.
17 Allah ya saurari Lai'atu, ta kuwa yi ciki ta haifa wa Yakubu ɗa na biyar.
18 Lai'atu ta ce, “Allah ya yi mini sakamako domin na ba da kuyangata ga mijina,” saboda haka ta raɗa masa suna Issaka.
19 Lai'atu ta sāke yin ciki ta kuwa haifa wa Yakubu ɗa na shida.
20 Sai Lai'atu ta ce, “Allah ya wadata ni da kyakkyawar baiwa, yanzu mijina zai darajanta ni, domin na haifa masa 'ya'ya maza shida,” ta raɗa masa suna Zabaluna.
21 Daga baya ta haifi 'ya mace, ta kuwa raɗa mata suna Dinatu.
22 Allah kuwa ya tuna da Rahila, ya saurare ta, ya buɗe mahaifarta.