18 Lai'atu ta ce, “Allah ya yi mini sakamako domin na ba da kuyangata ga mijina,” saboda haka ta raɗa masa suna Issaka.
19 Lai'atu ta sāke yin ciki ta kuwa haifa wa Yakubu ɗa na shida.
20 Sai Lai'atu ta ce, “Allah ya wadata ni da kyakkyawar baiwa, yanzu mijina zai darajanta ni, domin na haifa masa 'ya'ya maza shida,” ta raɗa masa suna Zabaluna.
21 Daga baya ta haifi 'ya mace, ta kuwa raɗa mata suna Dinatu.
22 Allah kuwa ya tuna da Rahila, ya saurare ta, ya buɗe mahaifarta.
23 Ta yi ciki ta haifa ɗa, ta ce, “Allah ya kawar da zargina,”
24 ta sa masa suna Yusufu, tana cewa, “Da ma a ce Ubangiji ya ƙara mini wani ɗa!”