20 Sai Lai'atu ta ce, “Allah ya wadata ni da kyakkyawar baiwa, yanzu mijina zai darajanta ni, domin na haifa masa 'ya'ya maza shida,” ta raɗa masa suna Zabaluna.
21 Daga baya ta haifi 'ya mace, ta kuwa raɗa mata suna Dinatu.
22 Allah kuwa ya tuna da Rahila, ya saurare ta, ya buɗe mahaifarta.
23 Ta yi ciki ta haifa ɗa, ta ce, “Allah ya kawar da zargina,”
24 ta sa masa suna Yusufu, tana cewa, “Da ma a ce Ubangiji ya ƙara mini wani ɗa!”
25 Bayan da Rahila ta haifi Yusufu, Yakubu ya ce wa Laban, “Ka sallame mu, domin mu tafi gidanmu a ƙasarmu.
26 Ka ba ni matana da 'ya'yana waɗanda na yi maka barantaka saboda su, ka bar mu mu tafi, ka dai san ɗawainiyar da na yi maka.”