38 Waɗannan shekaru ashirin da na yi tare da kai, tumakinka da awakinka ba su yi ɓari ba, ban kuwa ci ragunan garkenka ba.
39 Wanda namomin jeji suka yayyaga ban kawo maka ba, ni da kaina na ɗauki hasararsu. Ka kuma nemi abin da aka sace da rana ko da dare daga hannuna.
40 Abin da na zama ke nan, da rana na sha zafin rana, da dare kuwa na sha sanyi, ga rashin barci.
41 A waɗannan shekaru ashirin da nake cikin gidanka, na yi maka barantaka shekara goma sha huɗu domin 'ya'yanka mata biyu, shekara shida kuma domin garkenka, ka kuwa sauya ladana har sau goma.
42 Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”
43 Sa'an nan Laban ya amsa ya ce wa Yakubu, “'Ya'ya mata, 'ya'yana ne, 'ya'yansu kuma nawa ne, garkunan, garkunana ne, dukan abin da kake gani nawa ne. Amma me zan yi a wannan rana ta yau ga waɗannan 'ya'ya mata nawa, ko kuma ga 'ya'yan da suka haifa?
44 Zo mana mu ƙulla alkawari, da ni da kai, bari ya zama shaida tsakanina da kai.”