42 Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”
43 Sa'an nan Laban ya amsa ya ce wa Yakubu, “'Ya'ya mata, 'ya'yana ne, 'ya'yansu kuma nawa ne, garkunan, garkunana ne, dukan abin da kake gani nawa ne. Amma me zan yi a wannan rana ta yau ga waɗannan 'ya'ya mata nawa, ko kuma ga 'ya'yan da suka haifa?
44 Zo mana mu ƙulla alkawari, da ni da kai, bari ya zama shaida tsakanina da kai.”
45 Saboda haka Yakubu ya ɗauki dutse ya kafa shi al'amudi.
46 Yakubu ya ce wa iyalinsa, “Ku tattara duwatsu.” Sai suka ɗauki duwatsu, suka tsiba, suka kuwa ci abinci kusa da tsibin.
47 Laban ya sa masa suna Yegar-sahaduta, amma Yakubu ya kira shi Galeyed.
48 Laban ya ce, “Wannan tsibi shaida ce tsakanina da kai yau.” Saboda haka ya sa wa wurin suna Galeyed.