1 Yakubu ya ɗaga ido ya duba ke nan, sai ga Isuwa na zuwa da mutum arbaminya tare da shi. Sai ya raba wa Lai'atu da Rahila 'ya'yan, tare da kuyangin nan biyu.
2 Ya sa kuyangin da 'ya'yansu a gaba, sa'an nan Lai'atu sa'an nan Rahila da Yusufu a ƙarshen duka.
3 Shi kansa ya wuce gabansu, ya yi ta sunkuyar da kansa ƙasa sau bakwai, har sa'ad da ya kai kusa da ɗan'uwansa.
4 Amma Isuwa ya sheƙa ya tarye shi, ya rungume shi, ya faɗa a wuyansa, ya sumbace shi, suka kuwa yi kuka.
5 Sa'ad da Isuwa ya ta da idonsa ya ga mata da 'ya'ya, ya ce, “Su wane ne waɗannan tare da kai?”Yakubu ya ce, “Su ne 'ya'ya waɗanda Allah cikin alherinsa ya ba baranka.”
6 Sai kuyangin suka matso kusa, su da 'ya'yansu, suka sunkuya ƙasa.
7 Haka nan kuma Lai'atu da 'ya'yanta suka matso, suka sunkuya ƙasa, a ƙarewa Yusufu da Rahila suka matso kusa, su kuma suka sunkuya ƙasa.