9 Amma Isuwa ya ce, “Ina da abin da ya ishe ni, ɗan'uwana, riƙe abin da kake da shi don kanka.”
10 Yakubu ya ce, “A'a, ina roƙonka, in dai na sami tagomashi a idonka, to, sai ka karɓi kyautar da yake hannuna, gama hakika ganin fuskarka, kamar ganin fuskar Allah ne, bisa ga yadda ka karɓe ni.
11 Ina roƙonka, ka karɓi kyautar da na kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri matuƙa, gama ina da abin da ya ishe ni.” Da haka Yakubu ya i masa, Isuwa kuwa ya karɓa.
12 Sa'an nan Isuwa ya ce, “Bari mu ci gaba da tafiyarmu, ni kuwa in wuce gabanka.”
13 Amma Yakubu ya ce masa, “Shugabana, ai, ka sani 'ya'yan ba su da ƙarfi, ga kuma bisashe da shanun tatsa, ina jin tausayinsu ƙwarai da gaske. Idan kuwa aka tsananta korarsu kwana ɗaya, garkunan za su mutu duka.
14 Bari shugabana ya wuce gaban baransa, ni zan biyo a hankali bisa ga saurin shanun da yake gabana, da kuma bisa ga saurin yaran, har in isa wurin shugaba a Seyir.”
15 Sai Isuwa ya ce, “Bari in bar waɗansu daga cikin mutanen da suke tare da ni, a wurinka.”Amma Yakubu ya ce, “Ka kyauta ƙwarai, amma ba na bukatar haka, ya shugaba.”