13 'Ya'yan Yakubu, maza, suka amsa wa Shekem da mahaifinsa Hamor a ha'ince, domin ya ɓata 'yar'uwarsu Dinatu.
14 Suka ce musu, “Ba za mu iya yin wannan abu ba, mu aurar da 'yar'uwarmu ga marasa kaciya, gama wannan abin kunya ne a gare mu.
15 Ta wannan hali ne kaɗai za mu yarda, wato idan za ku zama kamarmu, ku yi wa dukan mazajenku kaciya.
16 Sa'an nan za mu ba ku auren 'ya'yanmu mata, mu kuma mu auro wa kanmu 'ya'yanku mata. Sai kuwa mu zauna tare da ku, mu zama jama'a ɗaya.
17 Amma idan ba ku saurare mu kun yi kaciya ba, sai mu ɗauki 'yarmu, mu kama hanyarmu.”
18 Hamor da ɗansa Shekem suka yi na'am da sharuɗan.
19 Saurayin kuwa bai yi jinkirin aikata batun ba, gama yana jin daɗin 'yar Yakubu. Shekem kuwa shi ne aka fi darajantawa a cikin gidan.