4 Sai Shekem ya yi magana da mahaifinsa, Hamor, ya ce, “Ka auro mini wannan budurwa ta zama matata.”
5 Yakubu kuwa ya ji an ɓata 'yarsa, Dinatu, amma 'ya'yansa maza suna tare da garken cikin saura, saboda haka Yakubu ya yi shiru har kafin su komo.
6 Sai Hamor mahaifin Shekem ya fita ya je wurin Yakubu, ya yi magana da shi.
7 'Ya'yan Yakubu, maza, kuwa sa'ad da suka komo daga saura, da suka ji yadda aka yi, sai suka hasala, abin ya ba su haushi ƙwarai, don Shekem ya yi aikin wauta ga Isra'ila da ya kwana da 'yar Yakubu. Gama irin wannan abu, bai kamata a yi shi ba.
8 Amma Hamor ya yi magana da su, ya ce, “Zuciyar ɗana Shekem tana begen 'yarku, ina roƙonku, ku ba shi ita aure.
9 Ku yi aurayya da mu. Ku ba mu 'yan matanku, ku kuma ku auri 'yan matanmu.
10 Sai ku zauna tare da mu, ƙasar kuma tana gabanku. Ku zauna a cikinta ku yi sana'a, ku sami dukiya.”