19 Waɗannan su ne 'ya'yan Isuwa, maza, wato Edom, da shugabanninsu.
20 Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Seyir Bahore, mazaunan ƙasar Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana,
21 da Dishon, da Ezer, da Dishan. Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, 'ya'yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.
22 'Ya'yan Lotan, maza, su ne Hori da Hemam, 'yar'uwarsa Timna ce.
23 Waɗannan su ne 'ya'yan Shobal, maza, Alwan, da Manahat, da Ebal, da Sheho, da Onam.
24 Waɗannan su ne 'ya'yan Zibeyon, maza, Aiya da Ana. Shi ne Ana wanda ya sami maɓuɓɓugan ruwan zafi a cikin jeji, a sa'ad da yake kiwon jakunan mahaifinsa Zibeyon.
25 Waɗannan su ne 'ya'yan Ana, Dishon da Oholibama 'yar Ana.