10 Amma sa'ad da ya faɗa wa mahaifinsa da 'yan'uwansa, sai mahaifinsa ya tsauta masa, ya ce, “Wane irin mafarki ne wannan da ka yi? Lalle ne, da ni da mahaifiyarka da 'yan'uwanka za mu sunkuya a gabanka har ƙasa?”
11 'Yan'uwansa suka ji kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe al'amarin cikin zuciyarsa.
12 Wata rana, da 'yan'uwansa suka tafi kiwon garken mahaifinsu a Shekem,
13 Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ashe, ba 'yan'uwanka suna kiwon garken a Shekem ba? Zo in aike ka wurinsu.”Sai ya ce masa, “Ga ni.”
14 Mahaifinsa ya ce, “Tafi yanzu, ka dubo lafiyar 'yan'uwanka da ta garken, ka kawo mini labarinsu.” Saboda haka, ya aike shi daga kwarin Hebron.Da Yusufu ya isa Shekem,
15 wani mutum ya same shi yana hange-hange cikin karkara. Sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?”
16 Yusufu ya ce, “Ina neman 'yan'uwana ne. Ina roƙonka ka faɗa mini idan ka san inda suke kiwon garkuna.”