15 wani mutum ya same shi yana hange-hange cikin karkara. Sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?”
16 Yusufu ya ce, “Ina neman 'yan'uwana ne. Ina roƙonka ka faɗa mini idan ka san inda suke kiwon garkuna.”
17 Mutumin ya ce, “Sun riga sun tashi daga nan, gama na ji sun ce, ‘Bari mu tafi Dotan.’ ” Saboda haka, Yusufu ya bi sawun 'yan'uwansa, ya kuwa same su a Dotan.
18 Da suka hango shi daga nesa, kafin ya zo kusa da su, sai suka ƙulla su kashe shi.
19 Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can yana zuwa.
20 Ku zo mu kashe shi yanzu, mu jefa shi cikin ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, sa'an nan mu ce, wata muguwar dabbar jeji ce ta kashe shi, sa'an nan mu ga yadda mafarkinsa zai zama.”
21 Amma sa'ad da Ra'ubainu ya ji, ya yi ƙoƙari ya cece shi daga hannunsu, yana cewa, “Kada mu raba shi da ransa.