8 'Yan'uwansa suka ce masa, “Ashe, lalle ne kai za ka sarauce mu? Ko kuwa, ashe lalle ne kai za ka mallake mu?” Sai suka daɗa ƙin jininsa domin mafarkansa da maganganunsa.
9 Shi kuwa sai ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa 'yan'uwansa, ya ce, “Ga shi kuma na sāke yin wani mafarki, na ga rana, da wata, da taurari goma sha ɗaya suna sunkuya mini.”
10 Amma sa'ad da ya faɗa wa mahaifinsa da 'yan'uwansa, sai mahaifinsa ya tsauta masa, ya ce, “Wane irin mafarki ne wannan da ka yi? Lalle ne, da ni da mahaifiyarka da 'yan'uwanka za mu sunkuya a gabanka har ƙasa?”
11 'Yan'uwansa suka ji kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe al'amarin cikin zuciyarsa.
12 Wata rana, da 'yan'uwansa suka tafi kiwon garken mahaifinsu a Shekem,
13 Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ashe, ba 'yan'uwanka suna kiwon garken a Shekem ba? Zo in aike ka wurinsu.”Sai ya ce masa, “Ga ni.”
14 Mahaifinsa ya ce, “Tafi yanzu, ka dubo lafiyar 'yan'uwanka da ta garken, ka kawo mini labarinsu.” Saboda haka, ya aike shi daga kwarin Hebron.Da Yusufu ya isa Shekem,