1 Aka kuwa gangara da Yusufu zuwa Masar. Sai Fotifar Bamasare sarkin yaƙin Fir'auna, shugaban masu tsaron fāda ya saye shi daga hannun Isma'ilawa, waɗanda suka gangaro da shi zuwa can.
2 Ubangiji yana tare da Yusufu, har ya zama mutum ne mai galaba a gidan maigidansa Fotifar, Bamasaren.
3 Maigidansa kuwa ya ga Ubangiji yana tare da shi, Ubangiji kuma yakan sa albarka ga aikin hannuwansa duka.
4 Don haka Yusufu ya sami tagomashi a wurinsa, ya zama mai yi masa hidima. Fotifar kuma ya shugabantar da shi a bisa gidansa, da bisa dukan abin da yake da shi.
5 Ubangiji ya sa wa gidan Bamasaren albarka sabili da Yusufu tun daga lokacin da Fotifar Bamasaren ya shugabatar da shi a bisa gidansa da dukan dukiyarsa. Albarkar Ubangiji na bisa dukan abin da yake da shi, na gida da na jeji.
6 Ya bar dukan abin da yake da shi a hannun Yusufu. Tun da ya same shi, ba ruwansa da kome, sai dai abincin da zai ci.Yusufu fa kyakkyawa ne mai kyan gani.