6 Ya bar dukan abin da yake da shi a hannun Yusufu. Tun da ya same shi, ba ruwansa da kome, sai dai abincin da zai ci.Yusufu fa kyakkyawa ne mai kyan gani.
7 Ya zamana fa, wata rana, sai matar maigidansa ta sa idonta kan Yusufu, ta ce, “Ka kwana da ni.”
8 Amma ya ƙi, ya kuwa faɗa wa matar maigidansa, ya ce, “Ga shi, tun da maigida ya same ni, maigidana ba ruwansa da kome na cikin gida, ya kuwa riga ya sa dukan abin da yake da shi cikin hannuna.
9 Bai fi ni iko cikin gidan nan ba, ba kuma abin da ya hana mini sai ke kaɗai, domin ke matarsa ce. Ƙaƙa fa zan aikata wannan babbar mugunta, in yi wa Allah zunubi?”
10 Ko da yake ta yi ta yi wa Yusufu magana yau da gobe, amma bai biye mata ya kwana da ita ko su zauna tare ba.
11 Amma wata rana, sa'ad da ya shiga cikin gida ya yi aikinsa, mazajen gidan kuma ba wanda yake gidan,
12 sai ta kama rigarsa, tana cewa, “Ka kwana da ni.” Amma ya bar rigarsa a hannunta ya gudu ya fita.