1 Adamu kuwa ya san matarsa Hawwa'u, ta kuwa yi ciki, ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Na sami ɗa namiji da iznin Ubangiji.”
2 Ta kuma haifi ɗan'uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne.
3 Wata rana, sai Kayinu ya kawo sadaka ga Ubangiji daga amfanin gona.
4 Habila kuwa ya kawo nasa ƙosassu daga cikin 'ya'yan fari na garkensa. Ubangiji kuwa ya kula da Habila da sadakarsa,