17 Kayinu ya san matarsa, ta kuwa yi ciki ta haifi Anuhu, ya kuwa gina birni ya sa wa birnin sunan ɗansa, Anuhu.
18 An haifa wa Anuhu ɗa, wato Airad. Airad ya haifi Mehuyayel, Mehuyayel kuwa ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifi Lamek.
19 Lamek ya auri mata biyu, sunan ɗayar Ada, ta biyun kuwa Zulai.
20 Ada ta haifi Yabal, shi ne ya zama uban mazaunan alfarwa, makiyayan dabbobi.
21 Sunan ɗan'uwansa Yubal, wanda ya zama uban makaɗan garaya da mabusan sarewa.
22 Zulai kuwa ta haifi Tubal-kayinu, shi ne asalin maƙeran dukan kayayyakin tagulla da na baƙin ƙarfe. Sunan 'yar'uwar Tubalkayinu Na'ama ne.
23 Lamek kuwa ya ce wa matansa, “Ada da Zulai, ku ji muryata, ku matan Lamek ku ji abin da nake cewa na kashe mutum domin ya yi mini rauni, saurayi kuma don ya buge ni.