14 Sai Fir'auna ya aika a kirawo Yusufu, da gaggawa suka fito da shi daga cikin kurkuku. Da Yusufu ya yi aski, ya sāke tufafinsa ya zo gaban Fir'auna.
15 Fir'auna kuwa ya ce wa Yusufu, “Na yi mafarkin da ba wanda ya san fassararsa, amma na ji an ce, wai kai, in ka ji mafarkin kana iya fassara shi.”
16 Yusufu ya amsa wa Fir'auna ya ce, “Ba a gare ni ba, Allah zai amsa wa Fir'auna da kyakkyawar amsa.”
17 Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, a cikin mafarkina ina tsaye a bakin Kogin Nilu,
18 ga shanu bakwai, masu sheƙi masu ƙiba suka fito daga cikin Nilu suna kiwo cikin iwa.
19 Sai waɗansu shanu bakwai ƙanjamammu, munana, ramammu, irin waɗanda ban taɓa ganinsu a ƙasar Masar ba, suka fito bayansu.
20 Sai ramammun, munanan shanun suka cinye shanun nan bakwai masu ƙiba na farko,