47 A cikin shekaru bakwai ɗin nan na ƙoshi, ƙasa ta ba da amfani mai yawan gaske,
48 sai ya tattara dukan abinci na shekarun nan bakwai da aka yi na ƙoshi a ƙasar Masar, ya kuwa tanada abinci cikin birane, a kowane birni ya tanada abinci daga karkarar da take kewaye da shi.
49 Sai Yusufu ya tsiba tsaba kamar yashin teku, har ya daina aunawa domin ba ta aunuwa saboda yawa.
50 Kafin kuwa shekarun nan na yunwa, an haifa wa Yusufu 'ya'ya biyu maza, waɗanda Asenat 'yar Fotifera, firist na On ta haifa masa.
51 Yusufu ya raɗa wa ɗan farin suna, Manassa, yana cewa, “Gama Allah ya sa ni in manta da dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.”
52 Na biyun kuma ya raɗa masa suna, Ifraimu, yana cewa, “Gama Allah ya wadata ni a cikin ƙasar wulakancina.”
53 Shekarun nan bakwai na ƙoshi da aka yi cikin ƙasar Masar sun cika,