14 Amma Yusufu ya ce musu, “Ai, kamar dai yadda na faɗa muku, magewaya ne ku.
15 Ta haka za a jarraba ku, da ran Fir'auna, ba za ku fita daga nan wurin ba, sai autanku ya zo nan.
16 Ku aiki ɗaya daga cikinku ya kawo ɗan'uwanku, amma ku, za a tsare ku, don a tabbatar da maganarku, ko akwai gaskiya cikinku, idan ba haka ba kuwa, da ran Fir'auna, lalle ku magewaya ne.”
17 Sai ya tura su cikin waƙafi har kwana uku.
18 A kan rana ta uku, Yusufu ya ce musu, “Abin da za ku yi in bar ku da rai ke nan, gama ina tsoron Allah,
19 sai ku bar ɗan'uwanku ɗaya a tsare a inda aka kulle ku. Idan amintattu ne ku, sauran kuwa su tafi su kai hatsi ga iyalanku mayunwata,
20 sa'an nan su kawo mini autanku. Ta haka za a tabbatar da maganarku, har a bar ku da rai.” Haka kuwa suka yi.