28 Ya ce wa 'yan'uwansa, “An mayar mini da kuɗina, ga shi nan a taiki!”Zuciyarsu ta karai sai suka juya suna duban juna, suna makyarkyata suna cewa, “Me ke nan da Allah ya yi mana?”
29 Sa'ad da suka zo wurin mahaifinsu Yakubu a ƙasar Kan'ana, suka faɗa masa dukan abin da ya same su, suna cewa,
30 “Mutumin, shugaban ƙasar, ya yi mana magana da gautsi, ya ɗauke mu a magewayan ƙasa.
31 Amma muka ce masa, ‘Mu amintattu ne, mu ba magewaya ba ne.
32 Mu sha biyu ne 'yan'uwan juna, 'ya'ya maza na mahaifinmu, ɗayan ya rasu, autan kuwa yana tare da mahaifinmu a yanzu haka a ƙasar Kan'ana.’
33 “Sai mutumin, shugaban ƙasar, ya ce mana, ‘Ta haka zan sani ko ku amintattu ne, ku bar ɗan'uwanku ɗaya tare da ni, ku ɗauki hatsi domin iyalanku mayunwata, ku yi tafiyarku.
34 Ku kawo mini autanku, da haka zan sani ku ba magewaya ba ne, amma amintattu ne, zan kuma ba ku ɗan'uwanku, ku yi ta ciniki a ƙasar.’ ”