35 Da zazzagewar tayakansu ga ƙunshin kuɗin kowannensu a cikin taikinsa. Sa'ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshin kuɗinsu, suka razana.
36 Sai Yakubu mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashi, ga shi, ba Yusufu, Saminu ba shi, wai kuma yanzu za ku ɗauki Biliyaminu, ga dai irin abubuwan da suka faɗo mini.”
37 Ra'ubainu kuwa ya ce wa mahaifinsa, “Ka kashe 'ya'yana biyu maza idan ban komo da shi ba, ka sa shi a hannuna, zan kuwa komo maka da shi.”
38 Amma ya ce, “Ɗana ba zai gangara tare da ku ba, ga ɗan'uwansa ya rasu, shi kaɗai kuwa ya ragu. Zai yiwu a kashe shi a hanya. Na tsufa ƙwarai ba zan iya ɗaukar wannan baƙin ciki ba, zai kashe ni.”