1 A halin yanzu, yunwa ta tsananta a ƙasar.
2 Sa'ad da suka cinye hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce musu, “Ku koma, ku sayo mana ɗan abinci.”
3 Amma Yahuza ya ce masa, “Mutumin fa, ya yi mana faɗakarwa sosai, ya ce, ‘Idan ba tare da autanku kuka zo ba, ba za ku ga fuskata ba.’
4 In za ka yarda ka aiki ɗan'uwanmu tare da mu, sai mu gangara mu sayo muku abinci.