24 Da mutumin ya kawo su gidan Yusufu, ya ba su ruwa, suka kuwa wanke ƙafafunsu, sa'an nan kuma ya bai wa jakunansu tauna,
25 sai suka shirya tsarabar, domin Yusufu yana zuwa da tsakar rana, saboda sun ji, wai zai ci abinci a nan.
26 Sa'ad da Yusufu ya koma gida, suka kawo tsarabar da suka riƙo masa cikin gida, suka sunkuya har ƙasa a gabansa.
27 Ya tambayi lafiyarsu ya ce, “Mahaifinku yana lafiya, tsohon nan da kuka yi magana a kansa? Yana nan da rai?”
28 Sai suka amsa, “Bawanka, mahaifinmu yana lafiya, har yanzu yana da rai.” Suka sunkuya suka yi masa mubaya'a.
29 Sai ya ɗaga idanunsa, ya ga ɗan'uwansa Biliyaminu, ɗan da mahaifiyarsa ta haifa, ya ce, “Wannan shi ne auta naku, wanda kuka yi mini magana a kansa? Allah ya yi maka alheri ɗana!”
30 Da Yusufu ya ji kamar zai yi kuka sabili da zuciyarsa tana begen ɗan'uwansa, sai ya gaggauta ya nemi wurin yin kuka. Ya shiga ɗakinsa, a can ya yi kuka.