1 Yusufu ya kasa daurewa a gaban dukan waɗanda suke a tsaye kusa da shi, sai ya ta da murya ya ce, “Kowa ya ba mu wuri.” Saboda haka ba mutumin da ya tsaya a wurin sa'ad da Yusufu ya bayyana kansa ga 'yan'uwansa.
2 Ya yi kuka da ƙarfi, har Masarawa suka ji, labarin kuwa ya kai gidan Fir'auna.
3 Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ni ne Yusufu. Mahaifina yana da rai har yanzu?” Amma 'yan'uwansa ba su iya ba shi amsa ba, gama sun firgita a gabansa.
4 Yusufu ya ce wa 'yan'uwansa. “Ku matso kusa da ni, ina roƙonku.” Suka matso kusa. Sai ya ce, “Ni ne ɗan'uwanku, Yusufu, wanda kuka sayar zuwa Masar.