19 Ka kuma umarce su ka ce, ‘Ku ɗauki kekunan shanu daga ƙasar Masar domin 'yan ƙanananku da matanku, ku ɗauko mahaifinku, ku zo.
20 Kada ku damu da kayayyakinku, gama abin da yake mafi kyau duka a ƙasar Masar naku ne.’ ”
21 Haka kuwa 'ya'yan Isra'ila suka yi. Yusufu kuma ya ba su kekunan shanu bisa ga umarnin Fir'auna, ya ba su guzuri don hanya.
22 Ga kowane ɗayansu ya ba da rigar ado, amma ga Biliyaminu ya ba da azurfa ɗari uku, da rigunan ado biyar.
23 Ga mahaifinsa kuwa ya aika da jakai goma ɗauke da kyawawan abubuwa na Masar, da jakai mata goma ɗauke da tsaba, da kuma abinci da guzurin hanya saboda mahaifinsa.
24 Ya sallami 'yan'uwansa. Da suna shirin tashi, sai ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya.”
25 Suka haura daga Masar, suka zo ƙasar Kan'ana zuwa wurin Yakubu mahaifinsu.