18 Waɗannan su goma sha shida, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Zilfa, wadda Laban ya bai wa Lai'atu, 'yarsa.
19 'Ya'ya maza, na Rahila, matar Yakubu, su ne Yusufu da Biliyaminu.
20 Asenat 'yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusufu Manassa da Ifraimu a ƙasar Masar.
21 'Ya'yan Biliyaminu, maza, su ne Bela, da Beker, da Ashbel, da Gera, da Na'aman, da Ahiram, da Rosh, da Muffim, da Huffim, da Adar.
22 Waɗannan su goma sha huɗu su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Rahila.
23 Hushim shi ne ɗan Dan.
24 'Ya'yan Naftali, maza, su ne Yazeyel, da Guni, da Yezer, da Shallum.