2 Daga cikin 'yan'uwansa kuma ya ɗauki mutum biyar ya gabatar da su a gaban Fir'auna.
3 Sai Fir'auna ya ce wa 'yan'uwan nan nasa, “Mece ce sana'arku?”Suka amsa wa Fir'auna, suka ce, “Ranka ya daɗe, mu makiyaya ne, kamar yadda iyayenmu suke.”
4 Suka kuma ce wa Fir'auna, “Ranka ya daɗe, mun zo baƙunci ne cikin ƙasar, gama ba wurin kiwo domin garkunan bayinka, gama yunwa ta tsananta a ƙasar Kan'ana. Yanzu muna roƙonka, ka yarda wa bayinka su zauna a ƙasar Goshen.”
5 Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Mahaifinka da 'yan'uwanka sun zo wurinka.
6 Ƙasar Masar tana gabanka. Ka zaunar da mahaifinka da 'yan'uwanka a ƙasa mai kyau, bari su zauna a ƙasar Goshen. In kuma ka san da waɗansu waɗanda suka dace a cikinsu, ka sa su su lura da shanuna.”
7 Yusufu kuwa ya shigo da Yakubu mahaifinsa, ya tsai da shi a gaban Fir'auna, Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka.
8 Fir'auna kuma ya ce wa Yakubu, “Nawa ne shekarun haihuwarka?”