6 Ƙasar Masar tana gabanka. Ka zaunar da mahaifinka da 'yan'uwanka a ƙasa mai kyau, bari su zauna a ƙasar Goshen. In kuma ka san da waɗansu waɗanda suka dace a cikinsu, ka sa su su lura da shanuna.”
7 Yusufu kuwa ya shigo da Yakubu mahaifinsa, ya tsai da shi a gaban Fir'auna, Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka.
8 Fir'auna kuma ya ce wa Yakubu, “Nawa ne shekarun haihuwarka?”
9 Yakubu ya ce wa Fir'auna, “Shekaruna na zaman baƙuncina, shekara ce ɗari da talatin, shekaruna kima ne cike kuma da wahala, ba su kuwa kai yawan shekarun kakannina ba, cikin baƙuncinsu.”
10 Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka, sa'an nan ya fita daga gaban Fir'auna.
11 Sai Yusufu ya zaunar da mahaifinsa da 'yan'uwansa, ya kuwa ba su mahalli a ƙasar Masar, cikin ƙasa mafi kyau a ƙasar Remesse, kamar yadda Fir'auna ya umarta.
12 Yusufu ya bai wa mahaifinsa da 'yan'uwansa da dukan iyalin gidan mahaifinsa abinci, bisa ga yawan 'ya'yansu.